Umar M Shareef – Kina Nesa

Umar M Shareef – Kina Nesa Lyrics Letra:
Kina nesa da idaniya
Kina kusa da zuciya

Kin yo nesa da idaniya ta
Kina kusa da zuciya

Jigon rayuwa soyayya ce

Na taɓa jin hakan sai na mance

Da naga mai kuka a So in ce kauce

Iya tunani na mai haka ya zauce

Yanzun gashi nan akan kai na, ina kuka kan Soyayya
Mun yiyo sabo da ke muna tare

Kullum in zo zance wurin ki in zanzare

Shaƙuwa ta kai Shaƙuwa aboki in ƙarƙare

Mun fara tunanin aure muja zare

Rashin ki yasa rana ya zam dare

Bana iya barci da idaniya

Duniya tayi ɗaci,
Rashin kine

Bana iya barci,
Domin ki ne

Na zam a kaɗaici,
Gani a jingine

Rayuwa ta kunci,
Yayi Kane-Kane

Yaushe hawaye zai bar zuba, Kizo ki tare aminiya.
Yaya zan yi in misalta soyayya

Yaya zan yi in fasalta soyayya

Ita ce ba’a saye da kuɗi duk dukiya

Ita ce mai gida na mulki shine zuciya

Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuya

Ya zubda hawayen idaniya
Kina nesa da idaniya
Kina kusa da zuciya

%d blogueiros gostam disto: